Trace Id is missing

Microsoft® Office Language Interface Pack 2013 – Hausa

Microsoft Office 2013 Language Interface Pack - Hausa yana ba da mahaɗin mai amfani da aka fassara ga yawancin afilikeshon ɗin Microsoft Office 2013.

Muhimmanci! Zaɓar wani yare da aka rattabo a ƙasa zai mauar da ɗaukacin shafin a wannan yaren.

  • Nau'i:

    2013

    Kwanan Watan Da Aka Wallafa:

    2013-03-15

    Sunan Fayil:

    languageinterfacepack-x64-ha-latn-ng.exe

    languageinterfacepack-x86-ha-latn-ng.exe

    Girman Fayil:

    12.7 MB

    12.6 MB

      Microsoft Office 2013 Language Interface Pack - Hausa yana ba da mahaɗin mai amfani da aka fassara don afilikeshon mai zuwa na Microsoft Office 2013:

    • Microsoft Excel® 2013

    • Microsoft OneNote® 2013

    • Microsoft Outlook® 2013

    • Microsoft PowerPoint® 2013

    • Microsoft Word® 2013


    • Ta amfani da Microsoft Office 2013 Language Interface Pack - Hausa, masu amfani da za su iya aiki a cikin sigogin harshe masu goyan baya na girkawar asali na afilikeshon ɗin Office da kuma duba umarni da zaɓuɓɓuka na afilikeshon ɗin a cikin - Hausa.

      Yayin girka Microsoft Office 2013 Language Interface Pack, fayilolin da ke ba wa masu amfani damar canza harshen mahaɗi na mai amfani ana yin kwafin su zuwa zangon ƙarshe na babban diski. Bayan girkawa, ana samun zaɓuɓɓukan ikon da daidaito na Microsoft Office 2013 Language Interface Pack - Hausa daga cikin afilikeshon na Office 2013 da kuma afilikeshon na Saitunan Harshe na Microsoft Office 2013.
  • Nau'ukan Tsarin Na'ura Da Ke Yi

    Windows 7, Windows 8

      Microsoft Windows 7 - 32 ko 64 bit OS
      Microsoft Windows 8 - 32 ko 64 bit OS
      Ƙarin bayani: Da fatan za a girka sabon Fakitin Sabis don Tsarin Aiki don tabbatar da mafi kyawun goyan baya ga harshen ku.

    Software Kowace sigar Office 2013 ta ɓangare ko mai cin gashin kanta wadda ta ƙunshi Microsoft Excel, Microsoft OneNote, Microsoft Outlook, Microsoft PowerPoint ko Microsoft Word ko za ta goyi bayan Microsoft Office Language Interface Pack 2013 - Hausa. Ƙarin bayani: Da fatan za a tabbatar da girka sabon Microsoft Office na Fakitin Sabis don samfuran Microsoft Office. Wannan zai tabbatar da mafi kyawun masaniyar mai amfani.

    Kwamfuta da mai Sarrafa Aiki Mai sarrafa aikin 1 GHz tare da goyan bayan SSE2 ko mafi girma; 2 GB RAM ko mafi girma

    Sararin Diski Ƙari ga sararin babban diski wanda afilikeshon na Office 2013 ya girka,
  • 3 GB na samammen sararin babban diski.

  • Duk sauran abubuwan baƙatun tsarin aiki daidai suke da na afilikeshon ɗin Office 2013 wanda kuke amfani da shi tare da Microsoft Office Language Interface Pack 2013 - Hausa.


  • Windows Language Interface Pack An ba da shawarar girka sabon Windows 7 Language Interface Pack ko Windows 8 don mafi kyawun goyan bayan harshe ga Tsarin Aiki da afilikeshon ɗin software naku.

    Saitunan Salon Allon Kwamfuta ad DPI An ƙirƙiri sigogin rubutu da yawa don mafi kyawun karantawa a salon 1366 x 768. Idan kuna fukantar wahalar karanta sigar rubutun harshen ku da fatan za a sabunta saitunan nuni ga wannan salon ko mafi girma in ya zama dole. Da fatan za a kula: muna ba da shawarar amfani da afilikeshon na Office 2013 a saitin Windows na asali DPI - 96 DPI. Yin amfani da saitin 120 DPI na iya haifar da ƙarancin masaniyar mai amfani na Office a cikin wasu afilikeshon na Office ta hanyar haɓaka girman Akwatin zaɓi na Office.

    Zaɓuɓɓukan Yanki da Harshe Bayan wannan kuma an ba da shawara cewa dukkan Zaɓuɓɓukan Yanki da Harshe a cikin Matattarar manhajar kwamfuta an saita su zuwa harshen Microsoft Office Language Interface Pack 2013 - Hausa.

  • Don girka wannan zazzagewar:
    1. Zazzage Fayil ɗin LanguageInterfacePack.exe ta hanyar danna Maɓallin zazzagewar (a sama) tare da adana fayil ɗin a babban diski.
    2. Danna-kan fayil na shirin LanguageInterfacePack.exe sau biyu a kan babban diskin ku don fara shirin Saitin tushe.
    3. Bi umarnin da ke kan allon don kammala girkawar.
    4. Da zarar an girka za a sami fayil ɗin karantani don Microsoft Office 2013 Language Interface Pack a C:\Fayilolin Shiri\Sanannun fayiloli\microsoft shared\OFFICE15\1128\LIPread.htm.
    5. Haɓakawar Office 2010 tare da Office 2010 Language Interface Pack ko kuma bugun farko zuwa Office 2013 tare da Office 2013 Language Interface Pack ba shi da goyan baya. Idan kuna da burin haɓaka tushen girkiwa na Office 2010 zuwa Office 2013 tare da Office 2013 Language Interface Pack lallai ne ku:
      • Cire girka Office 2010 Language Interface Pack.
      • Gudanar da saitin tushe na Office 2013 sannan a zaɓi nau'in haɓakawa.
      • Lokacin da aka kammala saitin tushe na Office 2013, girka a tsara fasalin Office 2013 Language Interface Pack.



    Kunna samfurin Office:
    Idan kuna fuskantar matsalar karanta gabaɗayan Kodin Girkawa a kan akwatin zaɓi na "Microsoft Office Activation Wizard", ko kuma gabaɗayan kodin baya fitowa daidai lokacin amfani da Microsoft Office 2013 Language Interface Pack naku, da fatan za a soke wizad ɗin sannan a sauya zuwa samfurin tushen harshen ku don kunna samfurin Microsoft Office ɗin.

    Umarni don amfani:
    Don sauya Mahaɗin Mai amfani naku zuwa harshen Microsoft Office 2013 Language Interface Pack – Hausa, bi waɗannan matakan:

    1. Mashigin manhaja Sinadarin Harshe na Microsoft Office 2013 daga Fara\Duk Shirye-shirye\Microsoft Office\Kayan aiki na Microsoft Office menu.
    2. Ƙarƙashin Zaɓi Nuna Harsuna da Taimako, a ƙarƙashin Nuna Harshe zaɓin harshen da ake buƙata sannan a danna Saita a matsayin maɓallin na Asali.
    3. Ƙarƙashin Zaɓi Gyara Harsuna, zaɓi harshen da ake buƙata sannan a danna Saita a matsayin maɓallin na Asali.
    4. Danna maɓallin YAYI.


    Saitunan harshe waɗanda kuka zaɓa za su yi aiki a gaba in kun kunna afilikeshon na Office ɗinku.
    Ƙarin bayani: Ba za a iya sauya Taimako zuwa Microsoft Office 2013 Language Interface Pack – Hausa ba. Taimako zai kasance a koyaushe cikin harshen asalin girkawa.
    Saita nuna taimako a koyaushe cikin jerin sunaye mai buɗuwa zuwa tushen harshe.

    Don cire wannan zazzagewar:
  • Dakatar da duk shirye-shiryen Microsoft Office.
  • Danna tambarin Shirye-shirye da Fasaloli a Matattarar Manhajar Kwamfuta na Windows.
  • A cikin zaɓuɓɓukan Cire girkawa ko Canza Shiri, danna Microsoft Office Language Interface Pack 2013 – Hausa a cikin akwatin shirye-shirye na Yanzu da aka girka , sannan a zaɓi maɓallin Cire Girkawa.
  • Bi umarnin a kan allon.