An wallafa: 30 ga Yuli, 2024
Zai fara aiki: 30 ga Satumba, 2024
Waɗannan sharuɗɗa ("Sharuɗɗa") sun shafi amfani da waɗancan samfurorin mai amfani na Microsoft, shafukan yanar gizo, da kuma sabis-sabis da aka jera a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa a nan (https://www.microsoft.com/servicesagreement#serviceslist) ("Sabis-sabis" ɗin). Ka yarda da waɗannan Sharuɗɗa ta ƙirƙirar wani asusun Microsoft, ta amfani da kake yi da Sabis-sabis, ko ta ci gaba da amfani da Sabis-sabis ɗin bayan an sanar da kai game da sauya waɗannan Sharuɗɗa.
1. Tsarin Sirrinka. Tsarin sirrinka yana da muhimmanci a gare mu. Daure ka karanta Bayanan Tsarin Sirri na Microsoft (https://go.microsoft.com/fwlink/?LinkId=521839) ("Bayanan Tsarin Sirri" ɗin) yadda ya bayyana nau'o'in bayanan da muke tara daga gare ka da kuma na'urorinka ("Bayanai"), yadda muke yin amfani da Bayananka, da kuma dalilolin shari'a da muke da shi don sarrafa Bayananka. Haka kuma Bayanan Tsarin Sirrin ɗin yana bayyana yadda Microsoft ke yin amfani da ƙunshiyarka, wanda yake sadarwarka tare da wasu; abubuwan da ka aika zuwa ga Microsoft ta hanyar Sabis-sabis ɗin; da kuma fayiloli, hotuna, daftarori, sauti, ayyuka na dijital, watsawa ta kai tsaye da kuma bidiyoyi da ka ɗora, ajiye, yaɗa, ƙirƙira, fito da, ko raba ta hanyar Sabis-sabis ɗin, ko shigarwar da ka miƙa domin fito da ƙunshiya ("Ƙunshiyarka"). A inda sarrafawa ya dogara da ƙunshiyar da kuma har iyakar da aka yarda ta doka, idan ka yarda da waɗannan Sharuɗɗa, ka amince Microsoft ya tara, yi amfani da kuma bayyana Ƙunsiyarka da kuma Bayananka yadda aka bayyana a cikin Bayanan Tsare Sirri ɗin. A wasu halaye, za mu samar da keɓaɓɓiyar sanarwa da kuma buƙatar yardarka kamar yadda yake a cikin Bayanan Tsare Sirri.
2. Taka Ƙunshiyar. Mafi yawan Sabis-sabis ɗinmu suna ba ka damar ƙirƙira, adana ko raba Ƙunshiyarka ko karɓar kayayyaki daga wasu. Ba mu a iƙirarin mallakar Taka Ƙunshiyar. Taka Ƙunshiyar zai kasance taka kuma kai ne kake ɗauka nauyinsa.
3. Dokar Ɗa’ar Ma’aikata. Kai ne kake ɗauka nauyin ɗa'arka da kuma ƙunshiyarka a lokacin da kake yin amfani da Sabis-sabis ɗin.
4. Amfani da Sabis-sabi da Tallafi.
5. Amfani da Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu. Sabis-sabis ɗin ƙila su ba ka damar samun iso ko mallakar samfurori, sabis-sabis, shafukan yanar gizo, hanyoyi, kayayyaki, wasanni, dabaru, haɗewa, bots ko manhajoji daga wasu mutane masu zaman kansu (kamfanoni ko mutane waɗanda ba Microsoft ba) ("Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu"). Mafi yawan Sabis-sabis ɗinmu haka nan suna taimaka maka samu, yin buƙatu ga, ko hulɗa da Manhajoji da kuma Sabis-sabis na Wasu kuma na iya ƙyale ko buƙata ka yaɗa Ƙunshiyarka ko Bayananka tare da irin waɗannan Manhajoji da kuma Sabis-sabis na Wasu, kuma ka fahimci cewa ta amfani da Sabis-sabis ɗinmu kana umartarsu da su samar maka Manhajoji da kuma Sabis-sabis na Wasu. Haka nan ƙila waɗannan Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu za su iya ƙyale ka ko buƙata ka adana Ƙunshiyarka ko Bayanai ba tare da mawallafin ba, mai samarwa, ko mai sarrafa Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu ɗin. Manhajoji da Sabis-sabis na wasun ƙila su gabatar maka da wata manufar tsare sirri ko su buƙace ka ka yarda da sharuɗɗa kafin ka iya saka ko amfani da Manhaja ko Sabis na Wasu. Duba sashe na 13.b don ƙarin sharuɗɗa don manhajoji da aka samu ta hanyar wasu Wuraren Adana da Microsoft ko rassansa ya mallaka kuma yake sarrafawa (da suka haɗa, amma, ba su taƙaita ga, Wurin Adana na Office, Microsoft Store a kan Xbox da kuma Microsoft Store a kan Windows. Za ka yi bitar sharuɗɗa da manufofin tsare sirri na wasu kafin samu, amfani, buƙata, ko haɗa Asusun Microsoft ɗinka ga duk wasu Manhajoji ko kuma Sabis-sabis na Wasu. Duk wasu sharuɗɗan wasu ba sa gyara waɗannan Sharuɗɗa. Microsoft ba ta bayar da lasisin duk wani hakkin mallaka na ilimi gare ka a zaman duk wasu Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu. Ka yarda ka ɗauki duk wani nauyi da ya taso daga amfani da waɗannan Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu da kuma cewa Microsoft ba ta da alhaki na duk wata matsala da ta taso ta amfani da su. Microsoft ba ta da alhaki gare ka ko wasu na bayani ko sabis-sabis da duk Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu suka samar.
6. Samuwar Sabis.
7. Sabuntawa ga Ayyuka ko Sofwaya ɗin, da kuma Canje-canje ga Waɗannan Sharuɗɗa.
8. Lasisin Sofwaya. Sai dai idan ya zo da wata wararriyar yarjejeniyar lasisin Microosft (misali, idan kana amfani da wata manhajar Microsoft da ta haɗa da wani ɓangare na Windows, a kokacin Sharuɗɗan Lasisin Manhajar Microsoft na Windows Operating System yake kula da wannan sofwaya), duk wata sofwaya da muka samar gare ka a zaman wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin ya shafi waɗanann Sharuɗɗa. Manhajoji da aka samu ta hanyar wasu Wuraren Adana da Microsoft ko rassansa ya mallaka kuma yake sarrafawa (da suka haɗa, amma ba su taƙaita ga, Wurin Adana na Office, Microsoft Store a kan Windows da Microsoft Store a kan Xbox) suna ƙarƙashin sashi na 13.b.i da yake ƙasa.
9. Sharuɗɗan Biyan Kuɗi. Idan ka sayi wani Sabis, ana sanya waɗannan sharuɗɗan biyan kuɗi ga sayayyarka kuma ka yarda da su.
10. Abun kwangila, Zaɓin Doka, da Wurin da za Warware Saɓani. Domin amfani da kake yi da Ayyukan masu alama-Skype na abokin ciniki na kyauta da kuma biyan kuɗi, idan kana da zama a waje da Turai, Gabas ta Tsakiya da kuma Afirka, waɗanda kake kwangila da su, kuma duk mahangi ga “Microsoft” a cikin waɗannan Sharuɗɗa suna nufin, Skype Communications S.à.r.l, 23 – 29 Rives de Clausen, L-2165 Luxembourg sai dai idan an bayyana dabam a ƙasa. Domin Ayyuka masu alamar-Skype na kyauta ko biyan kuɗi, idan kana da zama a waje da Turai, Gabas ta Tsakiya da Afrika, dokar Luzamburg ne take gudanar da fassarar waɗannan Sharuɗɗa da kuma diyyar ketarsu, ko me ne saɓanin aƙidun doka. Dokokin yardin ko ƙasar da kake da zama sune suke gudanar da duk sauran diyya (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci, da kuma diyya kan lahani). Idan kana da zama ne a waje da Turai, Gabas ta Tsakiya da kuma Afirka, kai da mu mun yarda da dokar ta musamman mara canzawa da kuma wuri na kotunan Luzamburg domin duk saɓani da yake taso daga ko dangane da Ayyukan masu alamar-Skype. Domin duk sauran Ayyuka, abun da kake yi wa kwangila, dokar mai sarrafa, da kuma wurin da za a warware saɓanin za su bayyana a ƙasa:
Wataƙila dokokin mai amfani na gida ɗinka za su buƙatar wasu dokoki na gida su gudanar da ko su ba ka damar warware saɓani a wani taro dabam duk da waɗannan Sharuɗɗa. Idan haka ne, zaɓen doka da kuma samarwar taro a cikin sashe na 10 za su sanya har yadda dokokin mai amfani na gida suka bari.
11. Yarjejeniyoyi.
Haja nan ka cancanji zaɓar wata ramuwa ko musanye na manyan kayayyaki nda suka kasa. Idan wata kasawa ta auku da kayayykin ko wani sabis ba ya haifar da wata babbar kasashi, ka cancanci samun gyara matsalar cikin lokaci. Idan bai gama ba ka cancanci ramuwa na kayayyakin da kuma soke kwangilar don sabis ɗin da kuma samun ramuwa don duk wani ɓangare da ba a gani ba. Haka nan ka cancanci ramuwar kuɗi da za a ba ka ga duk wata asara da ba a hange ta ba zuwa lalacewa daga kasawa a cikin kayan da kuma sabis-sabis.
12. Iyakance Sanadiyyar.
13. Sharuɗɗan Keɓaɓɓen-Sabis. Sharuɗɗan kafin da kuma bayan sashe na 13 an sanya su gaba ɗaya ga duk Sabis-sabis. Wannan sashe ya ƙunshi sharuɗɗan keɓɓɓen-sabis da suke ƙari ne ga sharuɗɗa na gaba ɗayan. Waɗannan sharuɗɗa suna aiki ne idan akwai wasu saɓani ga sharuɗɗa na gaba ɗayan.
14. Sauran abubuwa. Wannan sashe, da kuma sassa na 1, 9 (ga kuɗi wanda ya shiga kafin ƙarewar waɗannan Sharuɗɗa), 10, 11, 12, 15, 17 da kuma waɗanda sharuɗɗansu aka sanya bayan waɗannan Sharuɗɗa sun ƙare, duk wata ƙarewa ko soke waɗannan Sharuɗɗa ba ta shafar su. Har iyakanci da dokar da take shafa take yarda da, ya yiwu mu sanya waɗannan Sharuɗɗa, yi wa wajibcinmu ƙaramar kwangila a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa, ko yi wa hakkinmu ƙaramin lasisi na waɗannan Sharuɗɗa, gaba ɗaya ko wani ɓangare, a kowane lokaci ba tare da sanar maka ba. Ƙila ba za mu saka waɗannan Sharuɗɗa ko tura su zuwa wasu hakkoki don amfani da Sabis-sabis ɗin ba. Wannan ce ɗaukacin yarjejeniya tsakaninka da Microosft don amfani da Sabis-sabis ɗin. Wannan ya soke duk wata yarjejeniya ta baya tsakaninka da Microsoft da suka shafi amfani da Sabis-sabis ɗin da kake yi. Wajen shiga waɗannan Sharuɗɗa, ba ka dogara kan duk wani jawali, wakilci, garanti, fahimta, aiwatarwa, alƙawari ko tabbbaci fiye da waɗanda aka bayyana a cikin waɗannan Sharuɗɗa ba. An sanya duk sassa na waɗannan Sharuɗɗa zuwa iyakar da dokar da ta shafa ta ƙyale. Idan kotu ko wani alƙali ya ce ba za mu tilasta wani sashe na waɗannan Sharuɗɗa kamar yadda aka rubuta ba, ƙila mu iya musanya waɗannan sharuɗɗa tare da wasu sharuɗɗa masu kama zuwa iyakar tilastawa a ƙarƙashin dakar da ta shafa, amma ba za a sauya ragowar waɗannan Sharuɗɗa ba. Waɗannan Sharuɗɗa ne dominka da kuma alfanunmu. Waɗannan Sharuɗɗa ba alfanun sauran mutane ba ne, sai ga magada da kuma waɗannan Microosft ta sa. Kanun sashe don ddubawa ne kawai amma ba su da sakamako na shari’a.
15. Dole ne a Miƙa Ƙorafe-Ƙorafe Cikin Shekara Ɗaya. Duk wani ƙorafi da ya shafi waɗannan Sharuɗɗa dole ne a miƙa shi a cikin kotu (ko alƙali idan an sanya sashe na 10.d) cikin shekara guda daga ranar da za a fara miƙa ƙorafin, sai dai idan dokar ƙasarka ta buƙaci lokaci mai tsawo don miƙa ƙorafe-ƙorafe. Idan ba a miƙa cikin wannan lokaci ba, za a hana shi dindindin.
16. Dokokin Fitarwa. Dole ne ka bi duk dokokin gida da na waje na fitar kayayyaki ƙasashen waje da suka shafi manhajar da kuma/ko Sabis-sabis, wanda ya haɗa amma ba da iyakancewa ba da ƙasashe, masu amfani, da kuma nau’in amfani. Domin ƙarin bayani kan taƙaitawa na wurare da kuma fitar da kaya, ziyarci https://www.microsoft.com/exporting.
17. Keɓe Hakkoki da kuma Martani. Sai dai inda aka bayyana a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa, amma Microsoft ba ta baka wani lasisi ko duk wasu sauran hakkoki ko wasu iri a ƙarƙashin kowace lambar ƙira, yadda-ake, hakkin mallaka, sirrin kasuwanci, alamomin kasuwanci ko sauran hakkoki na ilimi mallakin Microsoft ko wanda take sarrafawa ko duk wani abu mai alaƙa, da ya haɗa amma ban da iyakancewa ga duk wani suna, alamar kasuwanci, tambari ko madadinsu. Idan ka ba wa Microsoft wata dabara, ƙuduri, shawara, ko wani martani, da ya haɗa, amma ban da iyakancewa ga dabaru na sababbin samfurori, kimiyya, talla, sunayen samfuri, martanin samfuri da kuma haɓaka samfuri ("Martani"), ka ba wa Microsoft, ba tare da wani biyan kuɗi ba, kuɗin shiga ko tilastawa gare ka ba, hakki na yi, samarwa, ayyukan kwaikwayon ƙirƙira, amfani, rabawa da kuma kasuwancin Martaninka ta kowace hanya da kuma kowane dalili. Ba za ka bayar da Martani da ya shafi wani lasisi da yake buƙatar Microsoft ta bayar da lasisin manhajarsa, fasaha ko daftarori ga wasu saboda Microsoft ta haɗa Martaninka a cikinsu.
Sanarwa da hanyoyin yin diyya kan keta haƙƙin mallakar ƙirar mutum. Microsoft tana mutunta haƙƙokin mallakar ƙirar mutum na wasu. Idan kana son aika wata sanarwar ketar haƙƙoƙin mallakar ƙirar mutum, da suke haɗa da diyyar ketar haƙƙin mallaka, daure ka yi amfani da hanyoyinmu na miƙawa Sanarwar keta (https://www.microsoft.com/en-us/legal/intellectualproperty/infringement) waɗanne hanyoyi suke kunshi waɗannan Sharuɗɗa. KAWAI BINCIKE DA SUKE DA MUHIMMANCI GA WANNAN HANYA NE ZA SU SAMU WATA AMSA.
Microsoft yana yin amfani da hanyoyi da aka bayyana a cikin Take na 17, Tsarin Doka na Amurka, Sashe na 512, da kuma inda ake sanya, Babi na III na Ƙa'idoji (EU) 2022/2065 don bayar da amsa ga sanarwar keta haƙƙoƙin mallaka ƙirar mutum. A lokuta da suka dace, haka kuma mai yiwuwa Microsoft ta hana ko ƙare asusu na masu amfani da ayyukan Microsoft waɗanda ƙila suka sake maimaita keta doka. Bugu da ƙari, a halayen da suke dace, wataƙila Microsoft ya dakatar da sarrafawa sanarwa ta wajen ɗaiɗaikun mutane ko ƙungiyoyin da suke sau da yawa miƙa sanarwa mara hujja. Wani ƙarin bayani ga hanyoyin da suke sanya don wani Sabis da aka bayar, da suke haɗa da sake dubawa mai yiwuwa na shawarwarin da Microsoft suke ɗauka a matsayin ɓangare na waɗannan hanyoyi, ana iya samun su a Sanarwar keta (https://www.microsoft.com/legal/intellectualproperty/infringement).
Sanarwa da kuma hanyoyi dangane da damuwa kan haƙƙin mallaka ƙirar mutum a cikin talla. Daure a yi bitar namu Jagororin Haƙƙin Mallaka Ƙirar Mutum (https://go.microsoft.com/fwlink/?LinkId=243207) dangane da damuwa da haƙƙin mallaka ƙirar mutum a kan tsarinmu na sadarwa na talla.
Sanarwar haƙƙin mallaka da alamar kasuwanci. An mallaka haƙƙoƙin Sabis-sabis ɗin © Microsoft Corporation da kuma/ko masu samarwa nasa, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. An mallaka duk haƙƙoƙi. Sharuɗɗan sun haɗa da Jagororin Microsoft na Alamar Kasuwanci da Alamar Samfuri (https://www.microsoft.com/en-us/legal/intellectualproperty/trademarks/usage/general.aspx) (yadda ake gyara lokaci-lokaci). Microsoft da kuma sunaye, tambarori, da duk alamomin samfurorin Microsoft, sofwaya, da kuma sabis-sabis ta yiwu alamomin kasuwanci wanda ba a yi wa rajista ba ko alamomin kasuwanci na taron kamfanoni na Microsoft da aka yi wa rajista a Ƙasar Amurka da kuma/ko sauran ƙasashe ne. Wannan da ya tafe wani jeri na alamomin kasuwanci na Microsoft wanda ba dukkansu ne nan ba https://www.microsoft.com/en-us/legal/intellectualproperty/trademarks/EN-US.aspx. Ainihin sunayen kamfanonin da kuma samfurori za su iya kasance alamomin kasuwanci na waɗanda suka mallaka su ne. Duk haƙƙoki da ba a bayar da su dalla-dalla a cikin waɗannan Sharuɗɗa ba an mallaka su. Wasu sofwaya da aka yi amfani da su a cikin wasu sabobin shafin yanar-gizo na Microsoft suna dogara ne a wani ɓangare aiki na Rukuni JPEG mai zama da kansu. Haƙƙin mallaka © 1991-1996 Thomas G. Lane. An mallaka duk haƙƙoƙi. Sofwayar "gnuplot" da aka yi amfani da ita a wasu sabobin yanar gizo na Microsoft suna da haƙƙin mallaki © 1986‑1993 Thomas Williams, Colin Kelley ne. An mallaka duk haƙƙoƙi.
Sanarwa kan lafiya. Microsoft ba ya bayar da shawara kan lafiya ko wasu shawarwarin kula da lafiya, binciken lafiya ko samun magani. Nemi shawarar likita ko wani ƙwararren mai kula da lafiya da duk wasu tambayoyi dangane da lafiya, abinci, kuzari ko shiri mai ƙara lafiya. Kada a taɓa yin sakaci ko jinkiri da ƙwararriyar shawara kan lafiya wajen nemanta saboda bayanin da ka sami iso gare shi ko ta hanyar Ayyukan.
Ambaton hannayen jari da kuma bayanan fihirisa (da ya haɗa da darajojin fihirisa). Bayanin Sha'anin Kuɗi da aka samar da shi ta Ayyukan don amfaninka na keɓe, mara kasuwanci ne kawai. Ƙila ba za ka iya amfani da wasu daga cikin bayanan sha'anin kuɗi ko makunan mai bayar da lasisi na wasu ba da suka shafi samarwa, ƙirƙiri, ɗaukar nauyi, kasuwanci, tallar ko garaɓasa na wasu na'urorin sha’anin kuɗi ko samfurorin zuba jari (misali, fihirisoci, sakamako, tsararrun samfurori, kuɗin zuba jari, kuɗin musayar kuɗi, wuraren zuba jari, da sauransu, inda farashi, riba da kuma /ko ƙarfin aikin na'urar ko samfurorin zuba jarin sun dogara kan, dangane da, ko an yi niyyar bin sawun kowane bayanan sha'anin kuɗi) ba tare da wata keɓaɓɓiyar rubutacciyar yarjejeniya tare da mai bayar da lasisi na wasu ɗin ba.
Sanarwar sha’anin kuɗi. Microsoft ba dillali ba ne/dila ko wani mai bayar da shawara kan hannun jari da aka yi wa rajista a ƙarƙashin dokokin kadarori na tarayyar ta Amurka ko sauran dokoki kan kadarori na wasu ɓangarori ba kuma ba ta ba wa ɗaiɗaikun mutane shawara kan zuba hannun jari, saye, ko sayar da kadarori ko sauran samfuroin sha’anin kuɗi ko ayyuka. Ba wani abu a cikin Sabis-sabis ɗin da ya kasance wani tayi ko jan hankali kan sayen ko sayar da wata kadara. Microsoft ko masu samar da ambaton hannun jari ko bayanan fihirisa ba su yaba ko shawarta wani keɓaɓɓun samfurori ko sabis-sabis na sha'anin kuɗi. Ba wani abu a cikin Sabis-sabis ɗin da aka yi niyyar ya zama ƙwararriyar shawara, da ya haɗa ba tare da iyakancewa ba, zuba jari ko shawara kan haraji.
Sanarwa game da Ƙa'idojin Bidiyo na H.264/AVC da kuma VC-1. Ƙila sofwayar ta haɗa da fasahar kodek ta H.264/AVC da kuma/ko VC-1 da bayar da lasisin ta wajen MPEG LA, L.L.C. Wannan fasara wani tsari ne don danƙara bayanai da bayanin bidiyo. MPEG LA, L.L.C. yana buƙatar wannan sanarwa:
AN SAMAR DA WANNAN SAMFURI NE A ƘARƘASHIN LASISI H.264/AVC, DA KUMA VC-1 SHAIDAR LASISIN KAYA DON KEƁAƁƁEN AMFANI DA KUMA AMFANI DA BA NA KASUWANCI BA ZUWA (A) ENCODE VIDEO BISA DACEWA DA INGANCI ("VIDEO STANDARDS") DA KUMA/KO (B) DECODE H.264/AVC, MPEG-4 VISUAL, DA KUMA VC-1 VIDEO WANDA AKA JUYA GA MAI KEƁAƁƁEN AMFANI KO AMFANI WANDA BA NA KASUWANCI BA DA KUMA/KO AKA SAMU DAGA LASISIN MAI SAMAR DA BIDIYO DON SAMAR DA WANNAN BIDIYO. BA LASISI DA AKA BAYAR KO ZA A SANYA DON WANI AMFANI DABAN. ƘILA ZA A IYA SAMUN ƘARIN BAYANI DAGA MPEG LA, L.L.C. DUBA SHAFIN YANAR-GIZO NA MPEG LA (https://www.mpegla.com).
Domin dalilan bayani kawai, wannan sanarwa bai iyakance ko hana amfani da sofwayar ba da aka samar da su a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa don amfanin kasuwanci na yau da kullum da suke kasance keɓaɓɓe ga wancan kasuwar wanda bai haɗa da (i) sake rabawa sofwayar ga wasu, ko (ii) ƙirar da kayan da suke da ƘA'IDOJIN BIDIYO da suke dace da fasahohi na rabawa ga wasu.
Sanarwa game da Ƙa'idar Bidiyo H.265/HEVC. Sofwayar tana iya haɗa da fasahar ɓoye bayanai na H.265/HEVC. Access Advance LLC yana buƙatar wannan sanarwa:
IDAN AKA HAƊA, ANA KULA DA FASAHAR H.265/HEVC A CIKIN WANNAN SOFWAYA TA WAJEN DIYYA ƊAYA KO FIYE DA HAKA NA HAƘƘIN ƘIRA na HEVC DA AKA JERA A: PATENTLIST.ACCESSADVANCE.COM. DANGANE DA YADDA KA SAMU SOFWAYAN, ZA A IYA BAYAR DA LASISI NA WANNAN SAMFURIN A ƘARƘASHIN TSARIN INGANTACCEN HAƘƘIN ƘIRA.
Idan aka girka wannan sofwaya a kan wata na'urar Microsoft, za a iya samu ƙarin bayanin lasisi a: aka.ms/HEVCVirtualPatentMarking.
SHARUƊƊAN DAIDAITACCEN LASISIN MANHAJA
MICROSOFT STORE. MICROSOFT STORE A KAN WINDOWS, DA KUMA MICROSOFT STORE A KAN XBOX
Waɗannan sharuɗɗan lasisi wata yarjejeniya ce tsakaninka da kuma mawallafin manhajar. Da fatan za a karanta su. Sun shafi manhajojin sofwaya da ka sauke daga Wurin Adana na Microsoft, Wurin Adana na Microsoft a kan Windows ko Wurin Adana na Microsoft a kan Xbos (wanda kowanne ake nuni da shi a cikin waɗannan sharuɗɗan lasisi a zaman "Wurin Adana"), da ya haɗa da duk wani sabuntawa ko ƙari ga wannan manhaja, sai dai idan manhajar ta zo da keɓaɓɓun sharuɗɗa, inda a wannan hali ake sanya waɗannan sharuɗɗa.
TA SAUKE KO AMFANI DA MANHAJAR, KO ƘOƘARIN YIN ƊAYA DAGA WAƊANNAN, KA AMINCE DA WAƊANNAN SHARUƊƊAN. IDAN BA KA AMINCE DA SU BA, BA KA DA WANI HAKKI KUMA DOLE NE BA ZA KA SAUKE KO AMFANI DA MANHAJAR BA.
Mawallafin manhajar yana nufin wanda yake baka manhajar lasisin, kamar yadda aka gano a Wurin Adana.
Idan ka bi waɗannan sharuɗɗan lasisi, kana hakkokin da suke ƙasa.
Wannan iyakancewa ta shafi:
Haka nan ya shafi idan:
Samfurorin da suke tafe, manhajiji da kuma sabis-sabis suna ƙarƙashin kulawar Yarjejeniyar Sabis na Microsoft, amma ƙila bza su samu a cikin kasuwarka ba.