Trace Id is missing

Sauye-Sauyen da aka samar ga Yarjejeniyar Sabis na Microsoft a taƙaice – 30 ga watan Satumba na shekarar 2023

Muna sabunta Yarjejeniyar Sabis na Microsoft, wanda ya shafi amfaninka na kayayyakin ko ayyukan mabuƙacin Microsoft a kan layi. Wannan shafin na ɗauke da muhimman sauye-sauyen da aka yi wa Yarjejeniyar Sabis na Microsoft a taƙaice.

Domin kallon dukkannin sauye-sauyen, to a daure a duba kammalallen Yarjejeniyar Sabis na Microsoft a nan.

  1. A sama, mun sabunta ranar wallafawa zuwa 30 ga watan Yulin shekarar 2023, sannan mun sabunta ranar fara aiki zuwa 30 ga watan Satumbar shekarar 2023.
  2. A sashen Sirrantawarku, mun faɗaɗa ma’anar “Ƙunshiyarku” domin ya haɗa da ƙunshiyar da ke samuwa sakamakon amfanin da za ku yi da sabis ɗin AI ɗinmu.
  3. A sashen Dokar Ɗa’ar Ma’aikata, mun ƙara harshe da zai kula da gudanar da sabis ɗin AI.
  4. A sashen Amfani da Sabis da Taimako, mun yi ƙare-ƙaren da aka zayyana a ƙasa:
    • Mun ƙara sashen Gyarawa da Tabbatarwa domin fayyacewa da taimaka wa masu amfani da sabis ɗin wane ƙara fahimtar waɗannan abubuwa.
    • Mun ƙara sashe da ke bayani game da ‘yancin da aka ba wa kwastomomi ‘yan Ostireliya da ke amfani da kayayyaki ko ayyuka da ke da alaƙa da Dokar Kare Mai Amfani da Kafafen Sadarwa, wanda ke ba wa mai amfanin damar ɗaukar Lauya ko Wakili da Doka ta Aminta da Shi domin fiskantar Microsoft a mai amfani da kayayykin Microsoft ɗin.
  5. A sashen Abun kwangila, Zaɓin Doka, da Wurin da za Warware Saɓani, an sabunta lamarin kwantiragi da ya shafi ɓangarorin da suke na kyauta na Microsoft Teams na Ostireliya.
  6. A sashen Sharuɗɗan Keɓaɓɓen-Sabis, mun yi ƙare-ƙare da sauye-sauyen da aka zayyana a ƙasa:
    • Mun ƙara bayani game da Dynamics 365 kasancewar za a iya kunna gwajin buɗe asusun wannan kaya ta hanyar tabbatarwar asusun Microsoft.
    • Mun sauya sashen Wuraren Bing domin yin ƙarin bayani game da lasisin mai akawun da zai iya ba wa kayan damar cimma abubuwan da ake so ya cimma.
    • Mun samar da sashe da ake kira “Ma’ajiyar Microsoft” wanda ya ƙunshi OneDrive da Outlook.com sannan ya haɗa da sauye-sauyen samfuri. Wannan ya shafi matsayin wurin ajiya na yanzu na abubuwan da aka ajiye cikin Outlook.com ta hanyar danganta shi da filin ajiya na OneDrive da kuma Outlook.com. Sannan an samar da mahaɗa ɗin da zai kai ga shafin da ke ƙunshe da ƙarin bayani.
    • Mun fayyace sashen Microsoft Rewards domin samar da ƙarin bayani da ya shafi shirin duniya, ƙarin taimako game da sanya masu amfani da asusun Microsoft kai tsaye da sauran sauye-sauyen shiri, da kuma ƙarin bayani domin ƙara fayyace shirin.
    • Mun ƙara sashe da ya shafi ayyukan AI domin sanya waɗansu iyakoki da ƙa’idoji da suka shafi Amfani da Ƙunshiyarka da ya danganci amfani da sabis ɗin AI.
  7. A sashen Sanarwowi, mun shirya domin sabunta matsayin sanarwa na wasu lasisi da kuma hakkokin kasuwanci.
  8. Cikin dukanin Sharuɗɗan, mun yi canje-canje domin inganta fahimta da kuma magance nahawu, kuskuren bugawa, da kuma irin al'amurran da suka shafi. Kuma mun sabunta sanyawar suna da kuma kalmomin haɗi.